Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira a ranar Talata ga bangarorin kasar Burundi da su nemi mafita kan rikicin kasar ta hanyar shawarwari.
Shugaba Buhari ya aike da wannan kira a yayin wata tattaunawa tare da tsohon shugaban kasar Burundi Pierre Buyoya a birnin Abuja, babban birnin Najeriya.
Ya ba da tabbatancin cewa, Najeriya za ta ci gaba da tallafawa shirin zaman lafiya, da kokarin zaman lafiya a nahiyar da kungiyar tarayyar Afrika (AU) , da tuni ta dukufa kan rikicin na Burundi.
"Ba za mu iya tilasta wa kasar Burundi karbar shawarar kungiyar AU ta tura sojojin wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar a wannan kasa ba, ganin cewa Bujumbura ta yi watsi da ita. Amma za mu ci gaba da taimakawa shirin shawarwari tsakanin bangarori masu gaba da juna dake kasar." in ji shugaban Najeriya.
Mista Buyoya, da ke matsayin babban manzon tawagar tarayyar AU game da Mali da yankin Sahel, ya nuna yabo kan rawar da Najeriya take takawa wajen maido da zaman lafiya a kasar Mali. Haka kuma, ya bukaci Najeriya da ta yi amfani da matsayinta domin kawo karshen rikici a Burundi, tare da yin kashedi cewa, wannan kasa na iya fadawa cikin wani yakin basasa. (Maman Ada)