Mataimakin shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana kudurin gwamnatin kasarsa na ganin ta samar da al'ummar da ba cutar AIDS a cikinta.
Mr Ramaphosa wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa gabanin bikin ranar yaki da cutar AIDS na duniya da zai gudana a ranar 1 ga watan Disamba, ya bayyana cewa, sun dauki matakai da dama na ganin an kawar da cutar ta AIDS kwata-kwata a tsakanin al'umma.
Don haka,ya yi kira ga daukacin 'yan kasar Afirka ta Kudu da su daura damarar ganin an kawar da cutar a cikin kasar da ma duniya baki daya.
Bayanai na nuna cewa, masu dauke da cutar AIDS sama da miliyan 3 ne a kasar Afirta ta Kudu ke amfani da maganin rage kaifin cutar baya ga kasancewarta kasar da ke kan gaba wajen shirye-shiryen yaki da cutar AIDS a duniya.
Baya ga matsalolin da masu fama da cutar ta AIDS ke fuskanta a kasar, ita ma kasar tana fama da kalubaloli da dama, gami da karuwar sabbin masu kamuwa da cutar da ake samu, musamman tsakanin mata da matasa.(Ibrahim)