in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rikicin Sudan ta Kudu ya kawo tseko game da shirin ci gaban kasar
2016-04-05 10:14:04 cri

Bisa dukkan alamu, kasar Sudan ta Kudu ba za ta cimma nasarar ayyana ta a matsayin kasar da ta yi ban kwana da ababan fashewa a karkashin kasa ba nan da shekara ta 2020, tun bayan da rikici ya barke a kasar a shekarar 2013, in ji mahukuntan kasar.

Jurkuch Barach, shugaban hukumar habaka albarkatun kasar ya bayyana cewa, a baya suna tsammanin za'a bayyana Sudan ta Kudu a matsayin wacce ta yi sallama da ababan fashewa da aka daddasa a kasar kafin nan da shekarar 2020, amma bisa la'akari da rikicin siyasa da ya addabi kasar tsawon shekaru 2 zuwa 3 da suka shude, da wuya a cimma wancan buri.

Jurkuch Barach ya fada wa 'yan jaridu a Litinin din da ya gabata a Juba cewa, bisa taimakon da MDD da sauran kasahen duniya ke bayarwa, an samu nasarar kawar da barazana a hanyoyin kasar masu nisan kilomita dubu 26, kuma dubban mutane sun fita daga cikin fargabar fashewar abubuwa.

Sai dai ya bayyana cewar, duk da irin nasarorin da aka samu game da share wurare a kasar, rikicin da ya kaure a kasar ya haifar da koma baya ta fuskar ci gaban kasa. A cewarsa, har yanzu ababan fashewar dake karkashin kasa sun kasance a matsayin babbar barazanar da al'ummar kasar ke fuskanta.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China