Shugaban Omar al-Bashir na Sudan ya ba da umarnin sake bude kan iyakar kasar da makwabciyarsa Sudan ta kudu.
Kamfanin dillancin labaran kasar SUNA ya ruwaito shugaba al-Bshir na umartar dukkan hukumomin da abin ya shafa, da su dauki dukkan matakan da suka wajaba na ganin sun aiwatar da wannan umarni.
A ranar Talata ce shugaban Salva Kiir Mayardit na Sudan ta kudu,ya umarni rundunonin sojojin kasar, da su ma su janye daga wuraren da suka ja daga a kan iyakar Sudan. Ya ce kamata ya yi dakarun su janye da a kalla tazarar mil 5 kudu daga kan iyakar da aka shata a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 1956, kamar yadda aka cimma a yarjejeniyar zaman lafiya ta 2005.
A watan Yunin shekarar 2011 ne kasar Sudan ta rufe kan iyakarta da Sudan ta kudu, sakamakon barin wutar da mayakan 'yan tawayen SPLM bangaren arewaci suka kaddamar a yankin Darfur na Sudan ta kudu.
Sudan dai na zargin makwabciyar Sudan ta kudu ta baiwa 'yan tawayen mafaka da taimakon kudi da nufin tayar da zaune tsaye a kan iyakarta.(Ibrahim)