Ministan harkokin waje da yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya na Sudan ta Kudu, Barnaba Marial Benjamin ya bayyana cewa, ziyarar magatakardan MDD na da muhimmanci kwarai ga kasar Sudan ta Kudu da jama'arta. Makasudin ziyararsa shi ne kalubalantar bangarori daban daban da su gudanar da yarjejeniyar yadda ya kamata.
Bayan haka, mista Benjamin ya bayyana cewa, mista Ban yana kokarin lallashin shugaban jam'iyyar adawa, Riek Machar da ya dawo birnin Juba tun da wuri, ta yadda za a iya kafa hadaddiyar gwamnatin rikon kwarya lami lafiya.
An ba da labarin cewa, Ban Ki-moon zai yi shawarwari da tawagar musamman ta MDD kan batun Sudan ta Kudu, da wasu jami'an wurin, da kuma wasu sarakunan gargajiya, domin sauraron ra'ayoyinsu, da rarraba musu ra'ayinsa. Daga bisani, Ban Ki-moon zai ci gaba da kai ziyararsa a kasar Kongo Kinshasa, domin yin bincike kan yanayin da ake ciki a fannin jin kai.(Fatima)