in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya nuna damuwa game da jinkirin kafa gwamnatin hadaka a Sudan ta kudu
2016-01-26 10:40:27 cri

Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya bayyana damuwa game da gazawar mahukuntan Sudan ta kudu na kafa gwamnatin hadaka a ranar 22 ga wata Janairun wannan shekara kamar yadda aka cimma.

Mr. Ban wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema kabarai, ya bayyana cewa kafa gwamnatin hadakar wani muhimmin bangare ne na aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma, wanda kuma shi ne zai dora harhashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Babban sakataren ya kuma nanata kudurin MDD na ci gaba da baiwa al'ummar Sudan ta kudu goyon bayan don ganin sun fita daga akuba da cin zarafin da suke fuskanta.

Mr. Ban ya kuma yi kira ga bangarorin biyu da su warware bambance-bambancen da ke tsakaninsu, Sannan ya bukaci kungiyar IGAD da ke shiga tsakani a rikicin kasar ta Sudan ta kudu, da ta tattauna batun tsekon da aka samu na kafa gwamnatin hadakar yayin taron kolin kungiyar AU da ke tafe.

A kwanakin baya ne dai shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu ya nada sabbin gwamnoni 28, a daidai gabar da tawagar 'yan tawayen kasar suka isa Juba, babban birnin kasar domin halartar tattaunawar kafa sabuwar gwamnati, yayin da bangarorin biyu ke zargin juna da karya tanade-tanaden da aka cimma a yarjejeniyar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China