in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya bukaci a tsaurara bincike game da amfani da nukiliya don yakar ta'addanci
2016-04-02 12:39:57 cri
A jiya Jumma'a, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci da'a dauki kwararan matakai game da binciken yadda ake amfani da sinadaren hada nukiliya wajen kaddamar da hare haren ta'addanci a duniya.

Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin gudanar da shawarwari tsakanin shugabannin kasashen duniya dake halartar taron koli karo na 4 na kwanaki biyu, game da tsaron Nukiliya a birnin Washington na kasar Amurka.

Da yake gabatar da kuduri game da matsayin kasar Sin dangane da shirin tsaron nukiliyar, shugaba Xi, ya bayyana cewar ya zama tilas duniya ta mai da hankali game da batutuwan da suka shafi binciken yadda ake samar da kayayyakin nukiliyar, da yadda ake sarrafa su, da jigilarsu da adana su dama yadda ake amfani da su.

Shugaban na Sin, ya yi kira da'a bullo da sabbin matakan yaki da ayyukan ta'addanci a shafukan yanar gizo.

Ya kara da cewar, ya zama tilas kasashen duniya su amince da juna wajen yakar ayyukan ta'addanci ta hanyoyin shafukan sada zumunta na intanet, da dokokin da suka shafi ta'ammali da kudi a wannan fanni.

Shugaba Xi ya ce, akwai bukatar a mai da hankali game da batutuwan da suka shafi muyasar bayanai tsakanin kasa da kasa da kuma inganta hadin gwiwa a sha'anin hukumomin tsaro.

Ya kara da cewar, ya kamata a mutunta bin doka da oda game da kiyaye sinadarin hada nukiliya don samun kariya, sannan ya ce hakki ne da ya rataya kan kasashen duniya ba tare da nuna wariya ba, ya kara da cewar, domin tabbatar da cimma wannan burin, ya zama wajibi a sanya hannu don amincewa da sabbin dokokin da aka tsara na tabbatar da tsaron nukiliya don gujewa sabbin haddura da za'a iya cin karo da su a nan gaba.

Bugu da kari, Shugaba shi ya ce, ayyukan ta'addanci babban makiye ne ga bil adama, inda ya bukaci yin hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya, da na shiyyoyi wajen dakile barazanar ayyukan ta'addanci.

Xi Jinping ya ce, za'a iya cimma nasarar magance yaduwar ta'addanci ta hanyoyi da dama, da suka hada da siyasa, da tattalin arziki, da al'adu da kuma hanyoyin diplomasiyya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China