
A ranar 29 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Czech Miloš Zeman a birnin Prague, inda shugabannin biyu suka nuna yabo ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Sa'an nan sun yin musayar ra'ayoyi kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Czech, da Turai, da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen tsakiya da gabashin nahiyar Turai, da kuma batutuwan kasa da kasa da na shiyya shiyya da ke jawo hankalinsu. Shugabannin biyu sun amince da inganta dangantaka da abokantaka dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)