
A jiya Alhamis 31 ga watan Maris, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na Amurka, Barack Obama a birnin Washington, inda suka yi musayar ra'ayi kan raya dangantaka tsakaninsu, da sauran harkokin shiyya shiyya da na duniya da suka fi jawo hankalin kowa. Bangarorin biyu sun amince da ci gaba da karfafa hadin gwiwa tsakaninsu, da yin mu'amala kan harokin duniya, da kara samun moriyar juna, ta yadda za a sa kaimi ga raya dangantaka kasashen biyu lami lafiya.(Fatima)