in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya halarci taron shugabannin kasashe 6 kan batun nukiliyar Iran
2016-04-02 08:47:54 cri
A ran 1 ga watan Afrilu, shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda ke Washington DC na kasar Amurka ya halarci taron shugabannin kasashe 6 kan batun nukiliyar kasar Iran, inda ya yi wani muhimmin jawabi.

A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya jaddada cewa, yarjejeniyar da aka kulla kan batun nukiliyar kasar Iran ta kasance tamkar wata muhimmiyar alama ce da ba safai ake ganinta ba, amma a waje daya, za a sha aiki sosai kan yadda za a iya aiwatar da ita kamar yadda ake fata. Dole ne mu cika alkawarin siyasa da muka yi, ta yadda za a iya aiwatar da yarjejeniyar kamar yadda ya kamata. Sannan kuma, ya kamata a kau da kalubalolin da mai yiyuwa ne za su kawo wa yarjejeniyar, domin tabbatar da ganin sauran matsaloli ba za su kawo illa ga aikin tafiyar da yarjejeniyar.

Bugu da kari, Xi Jinping ya jaddada cewa, har yanzu ba a samu kwanciyar hankali a duk duniya baki daya ba tukuna. Matsalolin da suke jawo hankulan al'ummomin duniya suna ta bullowa bi da bi. Sabo da haka, bai kamata a taba lokaci ba wajen daukar matakan tsaron duniyarmu gaba daya. An samu fasahohi da yawa daga aikin warware batun nukiliyar Iran. Da farko dai, yin shawarwari hanya ce mafi dacewa wajen daidaita matsalolin dake jawo hankulan jama'a. ko da yake a kan yi amfani da dogon lokaci wajen yin shawarwari, amma sakamakon da aka samu a yayin shawarwari yana samun karbuwa sosai. Sannan kara yin hadin gwiwa tsakanin manyan kasashe hanya ce mai amfani wajen daidaita irin wadannan matsaloli. Duk kasashen duniya suna kasancewa a duniyarmu nan tare, ya kamata manyan kasashe su zama muhimmin ginshiken ga kokarin daidaita matsaloli masu tsanani, kamar batun nukiliyar Iran. Bugu da kari, a yi kokarin daidaita matsaloli cikin adalci da kuma daidaito babbar ka'ida ce da ya kamata a bi wajen kokarin neman kulla yarjejeniya tsakanin kasa da kasa. Ya kamata a mai da hankali kan abubuwan da kowace kasa take kulawa. Ba a iya yin amfani da ma'aunoni iri biyu a lokacin da ake kokarin daidaita batutuwan kasa da kasa cikin adalci. Daga karshe dai, Xi Jinping ya jaddada cewa, shawarar siyasa da aka yanka muhimmin karfi ne ga kokarin ciyar da shawarwarin gaba. Ya kamata kowane bangaren da abin ya shafa ya kula da batu mafi muhimmanci, kuma a tsai da kuduri a lokaci mafi dacewa.

Dadin dadawa, Xi Jinping ya jaddada cewa, tun daga matakin farko zuwa na karshe, kasar Sin kasa ce da ke ba da gudummawa sosai wajen daidaita batun nukiliyar Iran kamar yadda ya kamata, kuma ta kan ciyar da shawarwarin gaba. Kasar Sin tana son hadin gwiwa wajen ingiza a aiwatar da yarjejeniyar baki daya ba tare da kasala ba, kuma za ta ba da sabuwar gudummawa ga kokarin tsaron duniyarmu gaba daya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China