in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya isa birnin Washington don halartar taron koli kan tsaron nukiliya karo na 4
2016-03-31 09:11:45 cri

A jiya Laraba ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Washington, hedkwatar kasar Amurka domin amsa goron gayyatar da takwaransa na Amurka Barack Obama ya yi, don halartar taron koli kan batun nukiliya karo na 4.

Taken taron na wannan karo shi ne "Inganta tsarin tsaron nukiliya a duniya". Mr. Xi zai halarci duk ayyuka a hukumance tare da yin muhimmin jawabi, don sanar da matsayin da Sin ke tsayawa game da tsaron nukiliya. A yayin taron, shugaban Xi zai halarci taron shugabannin kasashe 6 game da batun nukiliya na Iran.

Shugaba Xi ya isa birnin Washington bayan da ya kai ziyarar aiki a kasar Czech a hukunce.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China