in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da takwararsa ta kasar Koriya ta kudu
2016-04-01 11:09:20 cri

A jiya Alhamis a birnin Washington DC, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar kasar Koriya ta kudu Park Geunhye a, inda suka yi musayar ra'ayoyi game da huldar dake tsakanin kasashen biyu da kuma manyan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

Ban da haka kuma, shugabannin biyu sun yi musayar ra'ayi kan yanayin zirin Koriya. Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin ta nace ga batun kasancewar zirin Koriya da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a can, tana fatan za a daidaita batun ta hanyar yin shawarwari, ya kamata bangarori daban daban su gudanar da kudurin kwamitin sulhu na MDD a dukkan fannoni. Yin shawarwari ne daidaitaciyar hanya daya tak ta warware batu, kasar Sin tana son yin kokarin farfado da shawarwari bisa tsarin shawarwarin bangarori 6.

A nata bangare, Park Geunhye ya bayyana matsayin da kasar Koriya ke dauka kan batun zirin Koriya, sannan kuma zaka rinka tuntubar kasar Sin kan batutuwan da lamarin ya shafa.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China