in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Czech
2016-03-29 10:10:15 cri

A jiya Litinin da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Czech Milos Zeman a fadar shugaban dake karkara ta birnin Prague.

Shugabannin biyu sun shafe sao'i biyu suna yin shawarwari kan huldar dake tsakanin kasashen biyu, da huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Turai, da kuma sauran manyan batutuwa.

Xi Jinping ya jaddada cewa, tun da aka kafa huldar diplomasiyya shekaru 60 da suka gabata a tsakanin kasashen Sin da Czech, bangarorin biyu suna sada zumunta da hada kai a tsakaninsu yadda ya kamata.

Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar Sin tana nuna goyon baya ga yunkurin dunkulewar kasashen Turai waje guda, kuma Sin tana son kara yin hadin gwiwa tare da kungiyar EU da kuma dukkan kasashen Turai domin ba da gudummawa kan shimfida zaman lafiya da neman samun bunkasuwa a duniya.

A nasa bangare, Milos Zeman ya bayyana cewa, jama'ar kasar Czech da shi kansa sun dora muhimmanci sosai kan huldar dake tsakanin kasar Czech da kasar Sin, inda suka rika kokarin ingiza bunkasuwar huldarsu da kuma hadin gwiwarsu. Ya kara da cewa, kasarsa kawa ce ta aihini ga kasar Sin daga cikin kasashen kungiyar EU, tana son yi iyakacin kokari wajen ingiza huldar dake tsakanin kasar Sin da nahiyar Turai. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China