A yayin taron wanda babban sakatare na kwamintin Xi Jinping ya jagoranta an bayyana cewa, bunkasa harkokin sojoji da na jama'a ya zama wani babban sha'anin aikin kasar Sin, shi ne kuma babban shiri da kwamintin tsakiya ta jam'iyyar kwaminis ta tsara daga dukkan fannoni, kamata ya yi a inganta samun daidaituwar bunkasuwar tattalin arziki da harkokin tsaron kasa yadda ya kamata.
A gun taron, an nuna cewa tekun Yangtse uwar tekun al'ummar Sin, shi kuma ya zama wani jigon raya tattalin arzikin Sin. Don haka a lokacin da ake tsara shirin raya yanki, ya kamata a yi la'akari da kiyaye muhalli, domin bai kamata a raya shi fiye da kima ba.
Ya kamata a raya yankin bisa sharadin kiyaye muhalli, da inganta aikin raya yankin daga duk fannoni kuma cikin dogon lokaci, da kyautata ingancin raya aikin. Kamata ya yi a yi amfani da hanyoyin ruwa na kogin, don raya sana'o'i da kasuwanni.
A wajen taron har ila yau an lura ya kamata a tsara shiri daga manyan fannoni, don raya yankin dake kogin Yangtse da zai zama wani zirin tattalin arziki mai kyakkyawan muhalli, da daidaituwar bunkasuwar tattalin arziki.(Bako)