Kwamitin sulhun MDD ya shirya wani taro mai taken "Amfanin mata wajen yin rigakafi da daidaita rikice-rikicen Afirka", inda Liu Jieyi ya yi jawabin cewa, yanzu ana cikin mawuyacin hali na tabbatar da tsaro a duniya, musamman ma a nahiyar Afirka da yankin Gabas ta Tsakiya da sauransu. Rikice-rikice da barazana sun yi babbar illa ga rayuwar mata.
A sa'i daya, mata sun fara daukar karin nauyi na yin rigakafi da daidaita rikice-rikice a shiyya shiyya.
A sabili da haka, Liu Jieyi ya ce, kamata ya yi kasashen duniya su dauki kwararran matakai, su ba da kariya ga matan dake fama da rikici bisa iyakacin kokari. Sin tana dora muhimmanci kan yin hadin gwiwa da nahiyar Afirka a fannin mata, domin nuna musu goyon baya a fannonin siyasa, tattalin arziki, al'adu, tarbiya, kiwon lafiya da dai sauransu.
Sin na fatan yin aiki tare da sauran kasashen duniya, domin sa kaimi ga samun ci gaban mata a dukkan fannoni.(Fatima)