Wakilan matan Afrika da suka fito daga sassa daban daban na zaman rayuwa, tattalin arziki da siyasa na Afrika sun taru a ranar Litinin a cibiyar kungiyar tarayyar Afrika (AU) dake birnin Addis Abeba, hadkwatar Habasha, domin gudanar taruka na kwanaki uku, da zummar shirya wani karamin taro kan daidaici tsakanin maza da mata da kuma wayin kan mata.
Bangarorin suna halartar tarukan bisa tsarin shirya karamin taro na shekarar 2016 na kungiyar tarayyar Afrika (AU) kan 'yancin dan adam, tare da mai da hankali musammun ma kan 'yancin mata.
Karamin taro na daidaici tsakanin maza da mata zai tattauna muhimman ci gaban da aka samu ta fuskar zaman daidai wa daida tsakinin maza da mata, da kuma wayin kan mata, kimanta aiwatar da ayyukan da aka gudunar, musamman ma sanarwar shekarar 2015 kan wayin kan mata da kuma ci gaban ajandar shekarar 2063 a Afrika.
Makasudin taron shi ne na karfafa fadakarwa da bunkasa wata dabarar hadin gwiwa domin aiwatar da shirin shekarar 2016, shekarar 'yancin dan adam a nahiyar Afrika, musamman kan 'yancin mata.
Haka kuma taron zai tantance ci gaban da aka samu ta fuskar halartar mata a harkokin siyasa, tattalin arziki da na hukumomin shari'a, da kuma kokarin tantance muhimman kalubalolin dake hana halartar mata yadda ya kamata, tare da bullo da wasu dabaru domin gaggauta sanya hannu game da fada a jin mata a cikin harkokin siyasa, tattalin arziki da shiri'a. (Maman Ada)