Kwamitin kula da ci gaban mata na MDD a ranar Litinin din nan, ya bude taron tattaunawa game da ci gaban rayuwar mata karo na 60, domin nazartar muradin raya ci gaban kasashen duniya, inda za'a duba batun inganta rayuwar manyan mata da mata matasa.
Da yake jagorantar kaddamar da shirin, sakatare janar na MDD Ban Ki-moon, ya fada cewar, akwai abubuwa da dama dake wanzuwa a duniya na nuna bambamci ga mata, da 'yaya mata, da cin zarafin su, da kuma take hakkin su.
Shugaban taron Mogens Lykketoft, ya fada cewar, duk da kasancewar ci gaban da aka samu a shirin ci gaban mata da aka kaddamar a shekarar da ta gabata ba shi da yawa, amma akwai bukatar kasashen duniya su sa ido domin ganin an samar da daidaito tsakanin maza da mata, da kuma tsakanin kananan yara maza da mata a duniya, domin su ci moriyar damammaki na ci gaban duniya.
Taron zai gudana ne, tsakanin ranakun 14 zuwa 24 ga wannan wata, wanda zai mai da hankali kan batun ci gaban mata.(Ahmad Fagam)