in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aisha Buhari ta yi kiran da a samar da daidaito tsakanin jinsi
2016-03-08 20:42:01 cri
Uwar gidan shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari, ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su yi kokarin cike gibin dake akwai tsakanin maza da mata ta yadda za a samar da daidaito a bangaren rabon madafun iko.

Hajiya Aisha Buhari ta yi wannan kiran ne yau a Abuja yayin wani wasan kwaikwayo da aka shirya don murnar ranar mata ta duniya na wannan shekara, bikin da hukumar raya yankin Niger Delta ta shirya.

Hajiya Aisha Buhari wadda mataimakinyar gwamnan jihar Filato Mrs Pauline Tallen ta wakilce ta, ta bayyana cewa, mata na ba da gagarumar gudummawa a bangaren jin dadin jama'a, tattalin azriki, al'adu da siyasa. A cewarta, abu mai muhimmanci shi ne, Najeriya ta fara nuna abin misali ta hanyar karrama irin wadannan mata da suka taka rawar gani.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China