in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mata na ci gaba da fuskantar kalubale a fannin neman samun guraban ayyukan yi
2016-03-08 10:08:30 cri

Kungiyar 'yan kwadago ta kasa da kasa ta ba da rahoto game da mata 'yan kwadago na shekarar 2016, inda ta ce mata na ci gaba da fuskantar kalubale a fannin neman samun guraban ayyukan yi. A halin yanzu, yawan kudin shiga da mata ke samu yana da kashi 77 cikin dari ne kawai in an kwatanta da na maza.

Wannan rahoto ya yi bincike kan kididdigar da kasashe 178 suka yi a wannan fanni cewa, rashin daidaito a tsakanin mata da maza a fannin neman samun guraban ayyukan yi na ci gaba da kasancewa a duniya.

Ban da haka kuma, rahoto ya ce, mata na kokarin ganin ba su rasa samun guraban ayyukan yi ba, lamarin da ya fi tsanani a kasashen Larabawa da kasashen arewacin Afrika da kuma kudancin Asiya. Haka kuma rahoton ya nuna damuwa kan halin da mata ke ciki a yayin aiki.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China