Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya sake jaddada bukatar dake akwai, ta baiwa mata da yara mata cikakkiyar dama ta samun ilimi, da ayyukan yi, matakin da zai zamo jigo ga kariyar 'yancin su na rayuwa. Mr. Ban ya yi wannan tsokaci ne yayin kaddamar da taron makwanni biyu, na wakilan dandalin bunkasa tattalin arzikin mata karo na 60 a birnin New York.
Ya ce, wannan taro na gudana ne a gabar da masu ruwa da tsaki ke mai da hankali ga bunkasa manufar daidaito tsakanin jinsi, da inganta rayuwar mata. A wannan gaba ya dace mata da yara mata su ci gajiya iri daya da takwarorin su maza a fannin ayyukan yi, da kariyar shari'a, da jagoranci, tare da damar fada a ji.
Ban Ki-moon ya kara da cewa, an kafa wani kwamitin musamman yayin taron Davos na watan Janairun da ya shude, wanda zai gabatar da shawarwari da za su ba da damar hada ajandar ci gaban mata, da kudurorin ci gaba mai dorewa na shekara ta 2030. Hakan a cewar sa zai ba da tabbaci ga nasarar ci gaban tattalin arzikin mata, da damar su ta samun wakilci kamar yadda wakilan mata a MDD suka bukata.
Ana sa ran kwamitin zai fidda rahoton sa na farko cikin watan Satumbar dake tafe, kafin rahoton karshe da za a gabatar a watan Maris na shekara ta 2017.(Saminu)