Hukumomi biyu na MDD a ranar Talata suka sanar da wani sabon shirin da zai inganta kokarin da ake yi a kawo karshen aiurar da yara mata kanana da kuma kare miliyoyi daga yaran da ba su galihu a duniya baki daya.
Asusun kula da kananan yara UNICEF da asusun kula da yawan al'umma UNFPA suka sanar da hakan tare a lokacin bikin ranar mata ta duniya a wani kokari na kasashen duniya baki daya na hana yara mata kanana da auren wuri, da kuma goyon bayan kasashe 12 a nahiyoyin Afrika, Asiya, da yankin Gabas ta Tsakiya, inda aka fi samun irin wannan kwarai.
Sabon shirin na asusun biyu wato UNFPA-UNICEF da zai gaggauta daukan matakai na kawo karshen aurar da yara mata kanana, zai kunshi iyalai, unguwanni, gwamnatoci da kuma mata da nufin kawo karshen aurar da yara mata kanana nan da shekaru 15 masu zuwa, a cewar sanarwar da ake fitar wa manema labarai.(Fatimah)