in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Lin Yifu: "ziri daya da hanya daya" dama ce ga kasashe masu tasowa wajen cimma burin zamanintar kasa
2016-03-24 11:14:11 cri
Shugaba na musamman na kwalejin nazarin bunkasuwar kasa da kasa na jami'ar Peking kuma tsohon babban masanin tattalin arziki na bankin duniya sannan tsohon mataimakin shugaban bankin duniya Lin Yifu ya bayyana a gun taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar harkokin Asiya na Bo'ao na shekarar 2016 cewa, manufar "ziri daya da hanya daya" ta samar da dama ga kasar Sin kasancewa kasa mai arziki, kana ta samar da dama ga kasashe masu tasowa da dama da su cimma burin zamanintar kasa da kasancewa kasashe masu ci gaban tattalin arziki.

Lin Yifu ya bayyana hakan ne a gun taron shugabannin kafofin watsa labaru na taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa na Bo'ao.

Game da batun zuba jari ga kasashen Afirka da Sin ta yi, Lin Yifu ya bayyana cewa, koda yake jarin da Sin ta zuba wa kasashen Afirka ba ya da yawa sosai, amma yana karu da sauri. Ya yi imani cewa, bisa bunkasuwar Sin da manufar nan ta "ziri daya da hanya daya" da take aiwatarwa, idan kasashen Afirka suka rike wannan dama, za su kara samun ci gaba cikin sauri. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China