in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ta'addanci ya kasance kalubalen duniyar musulmi, in ji shugaban Mauritaniya
2016-03-24 12:13:32 cri

Shugaban kasar Mauritaniya Mohamed Ould Abdel Aziz ya bayyana cewa, ta'addanci na kasancewa wani babban kalubale da duniyar musulmi ke fuskanta, a yayin bude wani dandalin kasa da kasa bisa taken "Matsayin shugabannin kasashen kogin Sunna wajen yaki da kaifin kishin addini" a ranar Laraba a birnin Nouakchott.

A gaban shugabanni da limamai, shugaban ya jaddada cewa, kasar musulunci na fuskantar babban kalubale wanda a kan gabansa shi ne ta'addanci dake bada umurnin kashe mutane, da tozarta mutuncinsu da kwace dukiyoyinsu, bisa dogaro da fahimtar dake da akidar kaifin kishin addini da kaucewa, da janyo yake yake basasa a cikin wasu kasashen musulmi, da kawo illa ga tsaronsu da zaman lafiya.

Shugaban Mauritaniya ya bayyana cewa, yaki da ta'addanci da kaifin kishin islama na bukatar hada karfi da karfe da kokarin kowa, musammun ma taimakon manyan shugabannin addini wadanda nauyi ya rataya kansu wajen tabbatar da akidun gaskiya na tsarkakken addinin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China