Ban Ki-moon ya bayyana hakan ne a gun taron manema labaru da aka gudanar, bayan kammala shawarwari da firaminsitan kasar Lebanon Tammam Salam a birnin Beirut.
Mr. Ban ya ce kamata ya yi kasashen duniya su kara kokari wajen yaki da ta'addanci. Ya ce ya kamata sassan kasa da kasa su sa ido, tare da hada kai wajen tinkarar tsattsauran ra'ayin addini da 'yan ta'adda.
Kaza lika ya bayyana kawar da tushen ta'addanci, da na tsattsauran ra'ayi, a matsayin aikin mafi muhimmanci da ya dace a ci gaba da aiwatarwa. (Zainab)