in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 63 ne suka mutu sakamakon harin boma-bomai na kunar bakin wake a birnin Lahore na Pakistan
2016-03-28 13:25:43 cri

A daren jiya Lahadi 27 ga wata, kakakin gwamnatin lardin Punjab na Pakistan ya furta cewa, yawan mutanen da suka mutu sakamakon harin boma-bomai na kunar bakin wake a birnin Lahore ya karu zuwa 63, yayin da mutane 306 suka jikkata.

A daren jiya, an kai harin boma-bomai na kunar bakin wake a wani wurin yawon shakatawa dake birnin Lahore na lardin Punjab dake gabashin kasar Pakistan, wanda ya kashe mutane da dama tare da jikkata wasu da yawa.

Firaministan kasar, Mian Muhammad Nawaz Sharif ya yi Allah wadai da wannan danyen aiki, kuma ya bukaci a ba da jinya ga wadanda suka jikkata bisa iyakacin kokari.

Tuni dai wani kakakin reshen kungiyar Taliban a Pakistan ya bayyana wa kafofin yada labarai na wurin cewa, cewa suna da hannu a wannan hari. Kuma ya kara da cewa, wannan wani kashi ne dake cikin hare-haren da za su kai a bana.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China