Shugaba Obama ya nuna cewa, wannan yarjejeniya za ta taka muhimmiyar rawa wajen sanya wadannan makamai a karkashin kulawar kasashen duniya, ta yadda har ma za a lalata su a karshe. Mista Obama ya kara da cewa, Amurka za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tsakaninta da Rasha, Birtaniya, Faransa, MDD da kuma sauran bangarorin da abin ya shafa, a kokarin warware wannan batu yadda ya kamata.
A sa'i daya, shugaba Obama ya ce, idan gwamnatin Syria ta ki bin yarjejeniyar, ya kamata a hukunta ta. Idan kuma hanyar diplomasiyya ba za ta daidaita wannan matsala ba, Amurka za ta dauki matakai.
A ran 14 ga wata, sakataren harkokin waje na Amurka John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov sun daddale wata yarjejeniya dangane da hallaka makamai masu guba na Syria a Geneva bayan sun shafe kwanaki uku suna tattaunawa. (Fatima)