Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin da ma'aikatar cinikayya da masana'antu ta kasar Afirka ta Kudu sun yi wannan taro na mu'amalar ciniki a tsakanin kamfanonin kasashen biyu, domin ci gaba da habaka mu'amalar harkokin ciniki a tsakanin su da kuma daidaita bunkasuwar cinikin bangarorin biyu, bisa wannan lokacin musamman da za a kira taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka (FOCAC).
Kasar Afirka ta Kudu ita ce babbar abokiyar ciniki ta farko na kasar Sin a nahiyar Afirka, sannan kuma ita ma ta kasance kasa ta farko a Afirka da kasar Sin ta fi fitar da kuma shigar da hajoji.
Yarjejeniyoyin ciniki da kasar Sin da kasar Afirka ta Kudu suka kulla a wannan karo sun shafi fannonin sarrafa karafa, makamashi, likitanci, 'ya'yan itatuwa, abincin teku da dai sauransu. A wajen bikin, kamfanonin Sin 15 suka samu halarta, tare da kamfanoni sama da 50 na kasar Afirka ta Kudu. (Maryam)