Yau Alhamis 24 ga wata ne ake bikin bude taron shekara shekara na dandalin tattaunawar harkokin kasashen Asiya na Bo'ao, a birnin Bo'ao na lardin Hainan dake nan kasar Sin, inda cikin jawabin da ya gabatar, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya ce a bana, an cimma sakamako da dama, bisa wasu matakai da gwamnatin kasar Sin ta dauka, domin raya tattalin arziki, da kuma gudanar da kwaskwarima, lamarin da zai taimaka wa kasar ta Sin wajen samun bunkasuwar tattalin arziki cikin dogon lokaci mai zuwa.
Mr. Li ya ce ko da yake ana fuskantar kalubaloli da matsaloli da dama, amma tattalin arzikin kasar Sin na da makoma mai kyau.
Bugu da kari, Li Keqiang ya jaddada cewa, aikin neman ci gaba shi ne ke gaban komai ga kasar Sin, tana kuma mai da hankali kan inganci, da kuma saurin bunkasuwa, domin tabbatar da dauwamammen ci gaban kasar yadda ya kamata. (Maryam)