A daren ranar Jumma'ar nan 11 ga wata, an rufe taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar Asiya a garin Bo'ao na lardin Hainan a kasar Sin cikin nasara.
Zhou Wenzhong, babban sakataren kula da harkokin dandalin ya bayyana cewa, a bana yawan mahalarta taron ya karya matsayin bajimta a tarihin wannan taron shekara-shekara. Masasan ilmin siyasa, tattalin arziki da ilmi fiye da 1700 daga kasashe da yankuna guda 52 na duniya sun halarci taron, wadanda suka hada da minitocin wasu kasashe da shugabannin kungiyoyi daban daban fiye da 80, da manyan jami'ai na shahararrun kamfannonin duniya fiye da 150.
Mista Zhou ya yi bayanin cewa, an shirya taruruka iri daban daban guda 68 a bana, inda aka tattauna yadda za a raya kasashen Asiya mai dawamammen ci gaba, a kuma samu kirkire-kirkire a fannoni da dama. (Tasallah)