in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping zai halarci taron Bo'ao na bana
2015-03-19 19:49:54 cri
Yayin taron manema labaran da aka saba gabatarwa, a yau Alhamis kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei, ya sanar da cewa bisa gayyatar da aka yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai halarci bikin bude taron shekara-shekara, na tattauna na Bo'ao na shekarar 2015, inda zai gabatar da jawabi.

Haka kuma, bisa gayyatar da aka yi musu, shugabannin kasashen Uganda, Zambia, da kuma babban mataimakin firaministan kasar Rasha da wasu manyan jami'an kasa da kasa za su halarci taron.

Ban da haka kuma, bisa gayyatar da Xi Jinping ya yi musu, shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni, shugaban kasar Zambia Edgar Lungu, za kawo ziyarar aiki nan kasar Sin a yayin taron na Bo'ao. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China