Shugaban kasar Sin zai halarci taron shekara-shekara na tattaunawa na Asiya na Bo'ao
A yau 17 ga wata, mr. Zhou Wenzhong, babban sakataren kungiyar taron tattaunawa na Asiya na Bo'ao ya shirya wani taron manema labaru a nan Beijing, inda ya bayyana wa manema labaru yadda ake shirya ayyuka game da taron shekara-shekara tattaunawa na Asiya na Bo'ao na shekarar 2015. Mr. Zhou ya shelanta cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugabannin wasu kasashen duniya zai halarci bikin kaddamar taron, kuma yawan shugabannin kasashen duniya da za su halarci wannan taro zai wuce na tarukan Bo'ao da aka taba shiryawa a da.
Tun daga ranar 26 zuwa ta 29 ga watan Maris da muke ciki ne za a yi taron shekara-shekara na tattaunawa na Asiya a garin Bo'ao na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin. Babban taken wannan taro shi ne "Kokarin zama kungiyar hadin kai tsakanin kasashen Asiya a nan gaba". (Sanusi Chen)