Bugu da kari, Hua ta ce, Amurka ta taba kakabawa Cubar takunkumi sama da shekaru 50, amma a halin yanzu, suna kyautata dangantakar dake tsakaninsu cikin himma da kwazo, lamarin da ya dace da moriyar al'ummomin kasashen biyu, tare da kiyaye zaman karko da ci gaban yankin, shi ya sa kasar Sin take fatan Amurka da Cuba za su ci gaba da karfafa mu'amala a tsakaninsu, haka kuma, Sin ta yi kira ga kasar Amurka da ta kawar da takunkumin da take kakabawa Cubar bisa dukkan fannoni ba tare da bata lokaci ba.
Hua ta kara da cewa, a halin yanzu, abin da ya fi muhimmanci cikin harkokin dangantakar kasa da kasa shi ne, yin hadin gwiwa da cimma moriyar juna, kasar Sin da kasar Cuba suna da irin wannan dangantaka mai dogon tarihi, kuma kasar Sin za ta ci gaba da karfafa wannan dangantaka da Cuba a nan gaba ba domin sauran kasashe ba wadda kuma ba za a kawo illa kanta ba. (Maryam)