A cikin sanarwar da rundunar ta fitar, an ce, bisa rokon Abd-Rabbu Mansour Hadi, shugaban yanzu na kasar Yemen, rundunar ta sanar da tsagaita bude wuta a kasar Yemen tun daga ranar 15 ga watan Disamba da ya gabata domin kawo karshen rikicin da ake yi a kasar Yemen a siyasance da kuma kafa sharadin siyasa ga kokarin yin shawarwarin shimfida zaman lafiya a kasar. Amma dakarun Houthis da magoyan Ali Abdullah Saleh, tsohon shugaban kasar Yemen su kan saba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta sau da yawa, sun harba rokoki kan biranen kasar Saudiyya, har ma sun hana rundunar dakarun kawance da ta yi sufurin kayayyakin jin kai ga biranen kasar Yemen dake cikin hannunsu, bugu da kari, sun cafke da kuma hallaka jama'a dake zaune a yankunan da suka mamaye. Wadannan abubuwa sun bayyana cewa, dakarun Houthis da magoyan Saleh ba su da sahihanci ga shirin tsagaita bude wuta da yin shawarwarin shimfida zaman lafiya, suna son yin amfani da damar tsagaita bude wuta domin cimma burinsu kawai. (Sanusi Chen)