A ganawar da ya yi da manema labarai a wannan rana, ya ce Mr Ban musamman ya fi damuwa game da rahotannin dake nuna karuwan harin sama a wuraren da akwai mazauna da kuma gidajen jama'a a sana'a da suka hada da ofishin ciniki, zaurukan bikin aure da cibiyar makafi.
Mr. Ban ya tunatar da dukkan bangarorin a kan muhimmancin dake akwai na mutunta nauyin da ya rataya a wuyansu karkashin dokar kare hakkin bil adama wanda ya haramta kai hari kai tsaye a kan fararen hula ko muhallan su, in ji Dujjaric.
Magatakardar na MDD daga nan kuma ya yi kira ga dukkan bangarorin dake fada da juna a Yemen da su yi huldar cikin aminci da wakilin shi kuma manzon musamman a Yemen domin samar da daman aiwatar da wani zagayen tattaunawar ta ba da dadewa ba. (Fatimah Jibril)