in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a ci gaba da shawarwarin zaman lafiya na Yemen a 14 ga Janairu
2015-12-21 11:11:21 cri

An kammala shawarwarin zaman lafiya game da batun kasar Yemen da aka fara ranar Talata a Switzerland, kuma za a ci gaba da yin shawarwari na gaba a ranar 14 ga watan Janairu mai zuwa, in ji Ismail Ould Cheikh Ahmed, manzon musammun na MDD kan kasar Yemen, a yayin wani taron manema labarai a ranar Lahadi a birnin Bern.

Mun samu ci gaba sosai, amma duk da haka akwai saura, in ji manzon na MDD, bayan kwashe kwanaki shida ana tattaunawa tsakanin wakilan gwamnatin Yemen da kungiyoyin 'yan tawaye domin bullo da wata hanyar warware rikicin Yemen.

Haka kuma ya bayyana ci gaban da aka samu bisa tsarin sulhunta ricikin ta hanyar siyasa, dake dogaro bisa tushen kuduri mai lamba 2216 na kwamitin tsaro na MDD da ma wasu sauran muhimman kudurori, ta yadda za a iya kawo karshen rikicin da kuma kama hanyar kafa gwamnatin wucin gadi cikin lumana, kuma ya bayyana godiyarsa ga mahalarta taron kan halartarsu da kuma taimakon da suka bayar.

A cewar MDD, rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar dubun mutane da kuma tilastawa mutane kimanin miliyan 1,5 barin muhallinsu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China