Sanarwar ta bayyana cewa, kwamitin sulhun ya yi kira ga bangarori daban daban na kasar Yemen, da su komawa shawarwari ba tare da gindaya wani sharadi ba, su kuma warware matsalolinsu ta hanyar gudanar da shawarwari.
Kaza lika kwamitin tsaron ya bukace su da su kaucewa tsokanar juna, da sauran matakan da ka iya haifar da illa ga yanayin wucin gadi a fannin siyasar kasar. Mambobin kwamitin sulhun sun kuma yi tir da dukkanin wasu matakai na nuna karfin tuwo ga masu gudanar da shawarwarin.
Bisa shirin shiga-tsakani na MDD, bangarori daban daban da rikicin kasar Yemen ya shafa, sun fara gudanar da shawarwarin shimfida zaman lafiya tun daga ranar 15 ga watan nan, inda suka cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta kwanaki 7, wadda aka fara aiwatar da ita nan take.
Sai dai bayan kwana guda da daukar wannan mataki, sojojin gwamnatin kasar Yemen da dakarun Houthi, sun zargi da juna da sabawa yarjejeniyar tsagaita bude wutar, inda suka ci gaba da kaiwa juna hari.
Game da hakan, manzon musamman na MDD mai kula da batun Yemen Ismail Ould Cheikh Ahmed, ya sanar a ranar 20 ga wata cewa, za a sake komawa teburin shawarwari a tsakiyar watan Janairun shekarar dake tafe. (Zainab)