A jiyan ne dai ministan harkokin wajen kasar Jean-Marc Ayrault, da na harkokin gidan kasar Bernard Cazeneuve, suka isa birnin Abidjan fadar mulkin kasar Kwadebuwa, inda suka gana da shugaban kasar Alassane Ouattara, sa'an nan, suka ziyarci garin Grand Bassam dake kudancin kasar, inda dakarun sa kai suka kai hari ga masu yawon shakatawa a kwanakin baya, domin gabatar da ta'aziyar wadanda suka rasu sakamakon harin, ciki kuma har da 'yan kasar Faransa su hudu.
Haka kuma, a yayin ziyararsa a kasar, minista Cazeneuve ya sanar da cewa, kasar Faransa za ta tura sojojin rundunar musamman zuwa Ouagadougo fadar mulkin Burkina Faso, domin ba da shawara, da taimako yadda ya kamata, da kuma gaggauta gudanar da matakan dakile ayyukan ta'addanci, da dai sauran kalubalolin masu alaka da hakan a yankin yammacin Afirka. (Maryam)