in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan Faransa 4 sun rasu sakamakon hare-haren da aka kai Kwadebuwa
2016-03-15 11:07:27 cri
A jiya Litinin 14 ga watan nan ne shugaban kasar Faransa Francois Hollande, ya sanar da cewa 'yan kasarsa hudu na cikin wadanda suka rasu, sakamakon hare-haren da wasu 'yan bingida suka kaddamar a garin shakatawa na kasar Kwadebuwa, a wani wuri da ake kira Grand Bassam.

Bisa hakan ne kuma shugaban na Faransa, ya yi alkawari cewa kasar za ta karfafa aikin da take yi na yaki da ta'addanci a yammacin Afirka. A dai wannan rana, shugaba Hollande ya zanta da takwaransa na kasar Kwadebuwa Alassane Ouattara, game da hare-haren da aka kai Grand Bassam, inda ya nuna juyayi game da wadanda suka rasu. Haka kuma, shugaba Hollande ya ce, ya kamata kasashen dake fuskantar kalubalolin ta'addanci su karfafa hadin gwiwa tsakaninsu, musamman ma a yammacin Afirka.

Haka kuma, bisa labarin da aka samu, an ce, ma'aikatan hukumar yaki da ta'addanci ta kasar Faransa, da na babbar hukumar tsaron kasar sun riga sun isa garin da hare-haren suka auku domin fara bincike.

Bugu da kari, an ce, ministan harkokin tsaron kasar ta Faransa Jean-Yves Le Drianm ya bayyana cewa mai iyuwa ne, dakarun dake yankunan kasar Libiya masu alaka da kungiyar IS ne suka kutsa ta yankin tsibirin Lampedusa na kasar Italiya dake bahar Rum zuwa yankin na Kwadebuwa, wanda hakan ka iya haifar da sabon kalubalen ta'addanci a yankin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China