A ranar 10 ga wata, shugaban kasar François Hollande da firaministan kasar Manuel Valls da magajiyar birnin Paris Anne Hidalgo sun dasa wata bishiya a a filin jamhuriya dake birnin Paris, da cire kyalle ga dandamalin tunawa da mutanen da suka rasu.
Mahukuntan birnin Paris ya shirya wannan biki, don tunawa da mutane 17 da suka rasu sakamakon harin da aka kai ga cibiyar jaridar Charlie Hebdo a watan Janairu na shekarar 2015, da mutane 130 da suka rasu sakamakon harin ta'addanci da aka kai birnin Paris a ranar 13 ga watan Nuwambar bara. Mahukuntan birnin Paris sun gayyaci mutane sama da 1000 don halartar bikin, ciki har da wadanda suka tsallake rijiya da baya da dangogi da abokan wadanda suka mutu cikin hare-haren.(Bako)