A yayin da take kokarin amincewa da wannan shiri, MDD ta bayyana halin da ake ciki a kasar Cote d'Ivoire da cewar lamari ne dake barazana ga sha'anin tsaro a fadin yankin bakin daya.
To sai dai kwamitin MDD ya gamsu cewar, zaben shugaban kasar da aka gudanar cikin nasara a ranar 25 ga watan Octoban shekarar 2015, tamkar aza wani harsashen gina dawwamamman zaman lafiya ne a kasar Cote d'Ivoire wacce ta jima tana fuskantar tashe-tashen hankula.
Bugu da kari, kwamitin mai mambobi 15, ya yi na'am da ci gaban shirin wanzar da zaman lafiya na kasar, domin tabbatar da samun daidaito, da kwanciyar hankali, da tsaro da adalci da kuma farfado da cigaban tattalin arziki a kasar.
MDD ta yanke shawarar rage adadin jami'an aikin wanzar da zaman lafiyar ne bisa la'akari da rahoton da aka gabatarwar ofishin babban sakataren MDD a ranar 8 ga watan Disambar shekarar 2015.
An kafa tawagar UNOCI ne a shekarar 2004, domin samar da zaman lafiya da hada kan bangarorin da ba sa ga maciji da juna a kasar wanda aka rattaba hannu kansa tun a shekarar 2003. Sai dai a sakamakon barkewar wani sabon rikici bayan zaben shugaban kasar a shekarar 2010, UNOCI, ta ci gaba da aiki a kasar, domin kare fararen hular kasar da tallafawa gwamnatin kasar wajen fatattan 'yan tada kayar baya domin maido da zaman lafiya da kuma mutunta yancin bil adama a kasar. (Bilkisu)