Mista Kone dake tsokaci a cikin wata hira da aka watsa a kafofin rediyo da talabijin na kasa, ya nuna cewa sasanta 'yan kasa zai kasance daya daga cikin manyan ayyuka mafi mahimmanci na wa'adin shekaru biyar masu zuwa na shugaba Alassane Ouattara da ya sake lashe zaben shugaban kasa a karo na biyu.
Shugaba Alassane Ouattara zai maida hankali kan sauran matsalolin da suke kasancewa "kadangaran bakin tulu" da suke kawo zaton cewa 'yan Cote d'Ivoire ba a sasanta su ba, in ji mista Kone.
Idan aka yi la'akari da kalaman kakakin na gwamnati, a cikin watan Disamba mai zuwa, shugaba Ouattara zai gana da mambobin kwamitin sasanta 'yan kasa da biyan diyya ga wadanda rikici ya rutsa da su, sannan kuma da sakarunan gargajiya da shugabannin addinai.
Wannan muhimmin batu ne. Babban makasudin shi ne aiwatar da wani abin da ya dace domin ganin cewa 'yan Cote d'Ivoire na rayuwa cikin armashi da kuma hadin kai a dukkan fadin kasar Cote d'Ivoire, in ji mista Kone. (Maman Ada)