in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bada kyautar UNESCO-UNAM/Jaime Torres Bodet ta fannin ilimin zamantakewar al'umma da al'adu ta shekarar 2015
2015-12-09 13:13:20 cri

An zabi masanin kasar Cote d'Ivoire Bernard Binlin Dadie a matsayin wanda ya lashe kyautar UNESCO-UNAM/Jaime Torres Bodet ta fannin ilimin zamantakewa da al'adu ta wannan shekarar 2015, inda kuma ya samu wannan kyauta daga hannun babbar darektar UNESCO Irina Bokova, bisa amincewar kwamitin bada kyautar na kasa da kasa, a cewar wani labarin da ya fito daga cibiyar UNESCO a ranar Talata.

Bernard Binlin Dadier, wani babban masani ne wanda aka haife shi a shekarar 1916 a kauyen Assini na kasar Cote d'Ivoire, kuma na daga cikin 'yan takarar da suka fito daga kasashe daban daban 20. Bayan nazari sosai kan takardun 'yan takara, kwamitin bada kyauta na kasa da kasa ya amince bisa rinjaye da Bernard Binlin Dadier a matsayin wanda ya lashe kyautar ta shekarar 2015, wanda kuma ake daukarsa a matsayin wani babban marubucin Afrika da ya rubuta littattafai da dama da suka shahara sosai.

Mista Dadier ya taka rawa a wajen gwagwarmayar neman'yancin kasarsa, bayan'yancin Cote d'Ivoire a shekarar 1960, ya rike manyan mukamai na gwamnati da dama, ciki har da kujerar ministan al'adu a shekarar 1977 zuwa shekarar 1986. Mista Dadier ya bada gudunmuwa sosai ga kungiyar UNESCO inda kuma ya zama mamba tare da rike mukamin mataimakin shugaban kwamitin zartarwa na kungiyar daga shekarar 1964 zuwa 1972. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China