Cikin sanarwar, kwamitin sulhu na MDD ya mika ta'aziya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin, sanna ya nuna juyayi ga gwamnatocin kasashen Cote d'Ivoire, Faransa da dai sauran gwamnatocin kasashe na wadanda suka rasu sakamakon hare-haren.
Kaza lika, ya ce, kwamitin yana goyon bayan kasar Cote d'Ivoire da sauran kasashen dake yaki da ta'addanci, sa'an nan ya jaddada cewa, ya kamata a karfafa ayyukan kasa da kasa da na shiyya-shiyya domin yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda da masu tsattsauran ra'ayi. (Maryam)