Ministan ya yi bayani a yayin wata ganawa da hafsoshin sojojin kasar Cote d'Ivoire, cewar ta fuskar yaki da ta'addanci, kasar Cote d'Ivoire ta dukufa wajen rigakafin yaki da ta'addanci ba sai ya zo mata ba. A halin yanzu kasar ba ta cikin kasashen dake fama da hare-haren ta'addanci, amma duk da haka kasar na daukar nagartattun matakai domin kawar duk wani yunkurin ta'addanci.
A cewar mista Koffi Koffi, gaban barazanar matsalar tsaro da kuma wasu nau'o'in hare-hare a lokacin dake muke cikin karshen shekara, kusan jami'an tsaro dubu goma 16 aka watsa cikin kasar domin tabbatar da tsaron jama'a da dukiyoyinsu.
Muna son kwantar da hankalin al'ummomi da kuma murkushe duk wani nau'in barazana, in ji ministan, tare da kawo zancen musammun ma kan barazana a wuraren ibada, barazana kan iyakokin kasar da kuma ayyukan kungiyoyi masu dauke da makamai da aka fi kiransu da 'yan fashi da makami dake tare hanyoyi.
Jami'an tsaron Cote d'Ivoire suna cikin shirin ko ta kwana tun yau da kusan watannin da dama, inda kuma suka yi kira da al'ummomin kasa da su kara rubanya kokari wajen sanya ido kan duk wata barazanar ta'addanci da za ta kunno kai. (Maman Ada)