Yace kasar Sin ba za ta dogara ga fitar da kayayyaki zuwa ketare kawai domin samun karuwar GDP ba, yayin da jimillar kudin cinikayya na fidda kayyayaki zuwa ketare ba zai ba da gudummawa kamar yadda ya yi a da ba a cikin karuwar GDP. A cikin wannan yanayi kuma, amfani da manufar kudi da ta darajar musayar kudi domin sa kaimi ga cinikayyar fitar da kayyayaki zuwa ketare ba zai ba da taimako sosai ba, haka ma a fannin sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar.
Bayan haka, mista Zhou ya bayyana a fili cewa, Sin za ta ci gaba aiwatar da manufar kudi ta kaf da kaf idan ba za a fuskanci babbar matsalar kudi a nan gaba ba a Sin da ma duniya baki daya. (Fatima)