in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xu Shaoshi: Ana shirin fitar da mutane kimanin miliyan 55.75 daga talauci a Sin a yayin shirin shekaru biyar biyar karo na 13
2016-03-06 18:18:10 cri
Darektan hukumar raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin, Xu Shaoshi ya bayyana a yau Lahadi cewa, matsalar rayuwar jama'a da ake fi fama da ita a yayin aiwatar da shirin raya tattalin arziki da zaman al'umma na shekaru biyar biyar karo na 13 ita ce batun fitar da mutane daga talauci.

A lokacin taron aikin tattalin arziki na kwamitin tsakiyar JKS na shekarar 2015, yawan mutanen dake fama da talauci ya kai miliyan 70.17 a duk fadin kasar Sin. A kokarin da aka yi cikin shekarar guda, an fidda mutane kimanin miliyan 14.42 daga talauci.

A sabili da haka, a yayin shirin shekaru biyar biyar karo na 13, yawan mutanen da ke bukatar a fitar da su daga talauci ya ragu zuwa miliyan 55.75

Xu wanda ya bayyana hakan yau yayin taron manema labaru da aka shirya a gun taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da ke gudana, ya bayyana cewa, daftarin shirin shekaru biyar biyar karo na 13 ya fi mai da hankali kan kwararan matakan da za a dauka wajen kyautata rayuwar jama'a. A cikin shekaru biyar masu zuwa, Sin za ta ci gaba da kokarin fidda mutane daga talauci, ta yadda za ta cimma burin fidda duk al'ummar kasar daga talauci, da magance matsalar talauci a yankuna daban daban na kasar.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China