in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xu Shaoshi: Sin ba za ta dauki kwararen matakai don daidaita tattalin arzikin kasar cikin gajeren lokaci ba
2016-03-06 13:47:25 cri
Darektan hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin, Xu Shaoshi ya bayyana cewa, Sin ba za ta dauki kwararen matakai don daidaita tattalin arzikin kasar cikin gajeren lokaci ba.

Xu wanda ya bayyana hakan yau yayin taron manema labaru da aka shirya a gun taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ya bayyana cewa, tattalin arzikin Sin yana da karfin tunkarar duk matsalar da ka iya kunno kai, kuma yana da fifiko a fannoni biyar, wato yana da harsashi mai karfi na kayayyaki, da babbar bukatar kasuwanni, da babban yankin samun bunkasuwa, da kyautatuwar ingancin samar da kayayyaki, haka kuma tana da kwarewa wajen daidaita tattalin arziki daga manyan fannoni.

Ban da haka, mista Xu ya kara da cewa, muna da kwarewar tabbatar da ci gaban tattalin arzikin Sin a matakin da ya dace, sannan muna da tabbaci game da makomar ci gabansa.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China