A gun taron manema labaru da aka shirya a taron shekara shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin da ke gudana a nan birnin Beijing, Yi Gang ya bayyana cewa, darajar kudin RMB zai dore. Wannan kuwa saboda wasu dalilai guda uku. Da farko, tattalin arzikin Sin na ci gaba da bunkasa cikin sauri. Na biyu, akwai rarar kudin cinikayya na yau da kullum da dama, kuma yawan jarin da Sin ta zuba a ketare, da yawan jarin da aka zuba a cikin kasar daga ketare suna karuwa. Na uku, an samu kudaden kasashen waje da yawa da aka ajiye a cikin kasar.