A yayin bikin, firaministan gwamnatin kasar Sin Li Keqiang ya gabatar da wani rahoto game da ayyukan da gwamnatinsa ta yi a shekarar 2015, da ayyukan da gwamnatin za ta yi a shekarar 2016. A cikin rahoton, Li Keqiang ya nuna cewa, idan ana son samun kyakkyawar makoma, dole ne a yi namijin kokarin yin aiki. Dole ne duk al'ummomin kasar su dunkule waje daya a karkashin jagorancin kwamitin tsakiyar jam'iyyar JKS wadda ke karkashin shugancin babban sakatare Xi Jinping, ta yadda za a iya dukufa ka'in da na'in wajen ciyar da kasar Sin gaba domin kokarin cimma babban burin farfadowar al'ummomin kasar.
Wakilai kusan dubu 3, ciki har da shugaban kasar Xi Jinping da wasu shugabannin kasar suka halarci taron. (Sanusi Chen)