in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Koriya ta Arewa na shirya harba makaman nukiliya a kowane lokaci
2016-03-04 13:58:36 cri
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na kasar Koriya ta Arewa ya bayar a yau 4 ga wata, an ce, a kwanakin baya shugaban kasar Kim Jong-un, ya bada umurni ga sojojin jama'ar kasar da su kasance cikin shiri na harbar makaman nukiliya a kowane lokaci.

Wannan ne karo na farko da shugaban kasar Koriya ta Arewa ya bada damar yin hakan, tun bayan da kwamitin sulhun MDD ya zartas da kuduri dake shafar batun nukiliyar kasar.

Kim Jong-un ya bayyana umarnin nasa ne yayin da ake gwajin harba sabbin makaman roka. Amma labarin bai bayyana lokaci da wurin da aka yi gwajin ba.

Kwamitin sulhun MDD dai ya zartas da kuduri mai lamba 2270 game da batun nukiliya na kasar Koriya ta Arewa a ranar 2 ga wata, inda ya yi Allah wadai da matakin da kasar ta dauka na yin gwajin makaman nukiliya, da harbar tauraron dan Adam ta hanyar amfani da fasahar makamai masu linzami, kana ya bukaci kasar Koriya ta Arewa da ta yi watsi da shirin raya makaman nukiliya. Kaza lika kudurin ya gabatar da matakan sakawa kasar Koriya ta Arewa takunkumi, game da shirin ta na raya makaman nukiliya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China